Umurnin rufe babban ofishin hukumar bada katin zama dan kasan ya biyo bayan wasu matakai ne da hukumar ta dauka domin ganin an magance tururuwar mutane dake cincirindo a ofishin. An bude wasu cibiyoyi guda 20 a Babban Birnin Tarrayya, Abuja, domin a samu saukin aiwatar da rajistar ga masu bukata
Kadan daga cikin wuraren sune karamar hukumar Amak da ta Abaji da karamar hukumar Kwale, sai kuma karamar hukumar Gware sa’annan akwai Ajikawi da Korodo.
Darekta Janar na Hukumar bada katin zama dan kasan, Injiniya Aliyu Aziz, da ya sanar da bude wadannan cibiyoyin, ya ce wasu kamfanoni da suka kai kimanin 160 da aka bai wa lasisi a fadin kasar ne zasu gudanar da aikin.
Ya ce tuni kamfanonin suka fara shirye shirye na yin aikin, sun kuma sayi kayan aiki kamar motar bos da zasu bi mutane a masallatai da majami’u su yi musu rajista.
Baya ga wadannan Aliyu Aziz ya ce an kaddamar da wata manhaja mai suna mobile app wadda duk wani mai babbar waya zai iya amfani da ita wajen yin rajistar, kuma komin yawan layukan sim da mutum yake da su, zai iya yin amfani da lambarsa ta NIN ya yi rajistar su duka.
Wani abu da ya dauki hankali a wannan batu na yin rajistar lambar dan kasa shi ne gargadi da Hukumar EFCC ta yi cewa kar mutane su yi kuskuren sayar da lambar NIN din su ga Kowa, saboda ana iya amfani da lambar wajen yi rajistar wasu layuka daban da wanda mai lambar ya ke da su.
Gwamnatin Tarrayya ta umarci kamfanonin sadarwa da su kashe duk layukan tarho da ba a alakanta su da lambar NIN ba daga ranar 19 ga wannan wata. Yayin da wadanda suke rajista ba tare da lambar NIN ba Kuma, an ba su har zuwa ranar 9 ga Watan Fabrairu.
Ga dai rahoton Medina Dauda daga Abuja, Najeriya:
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: EFCC, NIN, Isa Ali Pantami, Nigeria, da Najeriya