NIAMEY, NIGER - Sama da million 40,000 na CFA ne aka kyasta cewa suna salwanta a kowace shekara a Nijer sanadiyyar ambaliyar ruwa ko sauran bala'o’in da ke afka wa gonaki, da filayen kiwo, da wuraren kamun kifi, lamarin da ke shafar miliyoyin mutane da galibinsu mazaunan karkara ne masu dogaro akan wadannan ayyuka. Dalili kenan gwamnatin wannan kasa ta fara hangen aiki da tsarin inshorar manoma kamar yadda abin yake a yanzu haka a kasashen Afrika da dama.
Ministan ayyukan jinkai na Nijer Alhaji Lawan Magaji ne ya bayyana hakan a wani taron manema labaran da kwamitin nazarin hanyoyin shimfida tsarin inshorar manoma ya kira.
Da yake magana da yawun kungiyar manoma da makiyaya ta Plate Forme Paysanne Djibo Bagna, kuma mamba a wannan kwamiti, ya fayyace irin alfanun da ke tattare da wannan tsari idan ya tabbata, yana mai cewa tsarin zai tallafa wa manoma su rage asara idan damina ba ta yi kyau ba.
Daukar inshora a kasashen Afrika musamman a Nijer wani tsari ne da mafi yawancin masu ababen hawa ke ganinsa tamkar na tilas don kauce wa haduwa da fushin hukuma, ba wai don kare kai daga asara ba.
To ko wane tabbaci kamfanonin inshora ke da shi kan cewa a wannan karon inshorar za ta amfani mai ita? Djibril Talatou, mamba a kawamitin inshorar manoma kuma shugaban kungiyar masu kamfanonin inshora, ya ce kasashe da yawa a Afrika sun gwada kuma suna ganin alfanun tsarin, a saboda haka don me Nijer baza ta bi sahu ba.
An dai bayyana cewa a yadda tafiya ta kama hanya akwai yiyuwar soma aiki da wannan tsari a shekarar 2023 .
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5