Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijer: Ana Taron Inganta Hanyoyin Kare Muhalli a Afurka Ta Yamma


Nijer: Ana Taron Inganta Hanyoyin Kare Muhalli a Afurka Ta Yamma
Nijer: Ana Taron Inganta Hanyoyin Kare Muhalli a Afurka Ta Yamma

Cibiyar nazari da binciken hanyoyin yaki da canjin yanayi a Afrika ta yamma WASCAL a takaice ta fara gudanar da taro a yau Laraba a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijer da nufin kara jan damarar yaki da illolin sauyin yanayi a kasashen kungiyar CEDEAO (ECOWAS).

Nijer: Ana Taron Inganta Hanyoyin Kare Muhalli a Afurka Ta Yamma
Nijer: Ana Taron Inganta Hanyoyin Kare Muhalli a Afurka Ta Yamma

Taron, wanda za a shafe kwanaki biyu ana gudanarwa, zai fara ne da yin bitar ayyukan cibiyar ta WASCAL na tsawon shekaru 10, wato daga kafuwarta kawo yau, kafin daga bisani mahalartan su tattauna akan sabbin hanyoyin da zasu bullo wa illolin sauyin yanayi a yammacin Afrika. Pr Hassirou Mohamed shi ne shugaban kwamitin gudanarwar cibiyar ta WASCAL, reshen Nijer, kuma ya yi karin haske.

Cibiyar mai kunshe da kasashe 11 na yankin Afrika ta Yamma na aiki kafada da kafada da jami’o'in gwamnatocin wadannan kasashe ta hanyar rassanta da nufin shigar da matasa gadan gadan cikin yaki da canjin yanayi. Har ila yau Pr Hassirou ya yi karin bayani.

Hakan ya sa gomman daliban da ke karantar kimiyar yanayi da dabarun tunkarar illolin canjin yanayi ke halartar wannan taro, ganin yadda tuni suka fara bullo da wasu hikimomin kare muhalli daga gurbata, wato fasahar samar da makamashi ta hanyar ruwa, abinda ake kira Hydrogene Vert, kamar yadda za a ji Karin bayani daga Hassan Ibrahim Tanimoune, dalibi a cibiyar WASCAL dake jami’ar Abdoul Moumouni .

Nijer: Ana Taron Inganta Hanyoyin Kare Muhalli a Afurka Ta Yamma
Nijer: Ana Taron Inganta Hanyoyin Kare Muhalli a Afurka Ta Yamma

Yaki da illolin canjin yanayi wani abu ne da a yau ya kamata matasan Afrika su maida hankali akansa saboda yadda abin ke kara zame wa wannan nahiya alkakai, inji Rouamba Prefina wata dalibar jam’iar Burkina faso.

Ta ce afrikawa mu ne baya wajen aikata abubuwan dake gurbata muhalli, amma kuma mun fi kowa dandana kudar wannan matsala, saboda haka ya kamata mu dauki wannan al’amari da mahimmanci mu tunkare shi babu kama hannun yaro. Saboda haka muke kiran gwamnatocin kasashenmu su ba mu goyon baya su tallafa mana domin akwai sabbin dubarun yaki da canjin yanayi.

Nijer: Ana Taron Inganta Hanyoyin Kare Muhalli a Afurka Ta Yamma
Nijer: Ana Taron Inganta Hanyoyin Kare Muhalli a Afurka Ta Yamma

Kasar Jamus ce ke daukar dawainiyar kudaden tafiyar da cibiyar WASCAL a dukkan kasashe 11 mambobinta, to amma duk da haka taron na Yamai wata dama ce da mahalartan za su yi amfani da ita don tayar da gwamnatocinsu daga barci akan maganar biyan kudaden tarbacen da ya kamata kowace kasa ta zuba a duk shekara.

Saurari rahoton Souleyman Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG