Sanin mahimmancin rawar da tsofafin sojoji ka iya takawa a fagen daga saboda da gogewa da kwarewar da suke da ita a kan sha’anin tsaro ya sa hukumomin Jamhuriyar Nijer bullo da wannan tsari na sake mayar da su kan aiki ta hanyar wata rundunar ko ta kwana a yayin da kasar ke neman hanyoyin magance matsalolin tsaron da suka addabe ta, Sergent Chef Moussa Tankandia shine matemakin hukumar kula da ‘yan mazan jiya ONAC.
Ya ce “Muna nan a kan shirye shirye mu na hada tsofaffin sojojin a yi musu rajista kuma zamu tura zuwa jihohi da garuruwa a yi rajistan wadnda suka cancanta. An riga an zakulo mutanen kirki cikin tsofaffin sojoji da ake bukata da za a basu horo na musamman saboda wasun su sun dade basu yi aiki ba”.
Wannan aiki da ke shafar sojoji da ‘yan sanda da jandarmomi da jami’an tsaron garde nationale da na Douane da jami’an tsaron gandun daji har ma da wadanda suka samu horon soja don aikin bautar kasa zai bada damar kafa rundunar da a kan iya turawa fagen daga a duk lokacin da bukata ta taso. Tsohon ministan tsaron kasa kuma dan majalisar dokokin kasa Kalla Moutari na mai bayani akan tasirin irin wannan runduna.
Ya ce wannan mataki ya samo asali ne daga tsarin kare ‘yancin kasa, saboda idan kasar ka na cikin wani bala’i ko wata matsala dole ne kowane dan kasa ya sadaukar da kansa ya kare kasarsa. Ganin yanda Nijer bata da isassun ma’aikatan tsaro, dole ne a ba wa duk wani dan kasa da ya yarda ya yiwa kasarsa yaki damar yin haka.
Bayyanar labarin kaddamar da wannan shiri ya tayar da tsumi a wajen wadanan tsofafin barade.
Shirin zai kunshi matasa ‘yan shekaru 18 a duniya zuwa mutanen da shekarunsu basu fice 65 ba, aikin da zai gudana a karkashin wasu tarin mahimman sharudan da zasu bada damar tantance wadanda suka cancanci shiga wannan sabuwar runduna koda yake kawo yanzu hukumomi ba su bayyana yawan askarawan da suke bukatar dauka ba.
Souley Moumouni Barma ya aiko mana Karin bayani daga birnin Yamai:
Your browser doesn’t support HTML5