Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Hana Tsallakawa Da Man Diezel Zuwa Kasashe Makwabta


Wannan kashedin, ya biyo bayan karancin man da kasar take fuskanta sanadiyyar yaki a kasar Ukraine, inda gangar man fetur ta harba daga dalar Amurka 80 zuwa 123 a yanzu haka.

- Hukumomin Jamhuriyar Nijer ta hanyar offishin ministan Man Petur da na offishin ministan kasuwanci, sun fiddo wata sanarwa da ke kashedi ga dukkan masu tsallakawa da man petur na DIEZEL ko Gazoil haka ma wuraren sayarda man a hukumance da kar su kara kudaden mai ko su kuka da kan su.

A cikin daren jiya ne ma'aitun ministocin kasuwanci da na man petur na jamhuriyar Nijer, suka fiddo sanarwar yin kashedi wa yan kasar da ma duk masu tsallakawa da man petur na gazoil ko diesel izuwa kasahen wajje ko makwabtan jamhuriyar Nijer.

Wannan kashedin, ya biyo bayan karancin man da kasar take fuskanta sanadiyyar yaki a kasar Ukraine, inda gangar man fetur ta halba daga dalar Amuruka 80 zuwa 123 a yanzu haka. yayin da ma'aikatar da ke da alhakin sayarda man ta kasar cewa da SONIDEP tace a iyaka da Tarrayar Najeriya, matasa ne ke zuwa a tasha - tasha suna cika jarka jarka suna shiga da su a Najeriya saboda man ya hauhawa a can, saboda shigowa da tataccen man da Najeriya ke yi, ganin ya hauhawa a kasuwar duniya da man karamcin sa saboda yaki Rasha da Ukraine.

Na yi Magana da wani mai sayarda man Diesel a bayan fage a garin Birni N'Konni inda yayi mini bayyanin halin da a ke ciki.

Wannan lamarin na rashi ko karamcin man Diesel a Nijer, ya sa matafiya cikin wani halin rabbana ka wadata mu. kamar yanda wadansu direbobin manyan motoci da na hadu da su a garin Birni N'Konni suka yi mini bayyani.

Ita dai gwamnatin da jamhuriyar Nijer, ba'ada bayan hana tsallakawa da man na Diesel, ta kara yin kashedi ga masu tashar mai da kar su kuskura su kara kudin mai ko kuma su kuka da kan su.

Saurari rahoton cikin sauti daga Harouna Mamane Bako:

Gwamnatin Nijer Ta Hana Tsallakawa Da Man Diezel Zuwa Makwabta Ko Kasashen Waje
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG