NIJAR: Za A Yi Amfani Da Fasahar Zamani Wajen Samar Da Ruwan Sama

giza gizai kan wani birni

Hankulan mazauna yankunan karkara a Jamhuiryar Nijar ya fara kwantawa bayan da ma’aikatar hasashen yanayin kasar ta kaddamar da ayyukan harbin giza-gizai domin samar da wadatar ruwan sama musamman a yankunan da aka fuskanci barazanar fari a watan yulin da ya gabata.

Wannan wata dubara ce da masana kimiya suka bullo da ita a matsayin wani bangare na matakan yaki da illolin canjin yanayi.

Daukewar ruwan sama a wani lokacin da ake tsakiyar ayyukan noman damana wani mummunan al’amari da ya fara wanzuwa a ‘yan shekarun nan a Nijer kasar da ke tsakiyar yankin Sahel wace galibin jama’arta ke dogaro da yanayin damana don tanadin abincin mutane da na dabobi saboda haka shugaban kasa Mohamed Bazoum ya umurci masana sha’anin kimiyar sararin samaniya su samar da hanyoyin magance wannan matsala mafarin kaddamar da ayyukan harbin giza gizan ta hanyar amfani da wasu sinadaran musamman.

Dr Katchallou Laouan Gaptchia shine babban darektan ma’aikatar hasashen yanayi ta kasa.

Kungiyoyin ma’aikatan karkara sun bayyana gamsuwa da wannan mataki ko da yake abin ya zo cikin yanayin ba-za-ta a cewar shugaban kungiyar Plateforme paysanne Djibo Bagna.

Sai dai kwararru a wannan fanni sun tabbatar da cewa aiki ne dake gudana cikin hikima da lissafi a kimiyance.

Binciken masana ya yi nuni da cewa giza gizai a akasarin kasashen Afrika kan fito daga gabas su nufi yamma, a bisa la’akari da wadanan bayanai ya sa ma’aikatar hasashen yanayi a yayin wannan aiki na harbin giza gizai ke fara shirin daga jihohin gabashi da arewacin kasa.

Daga farkon watan nan na Agusta kawo yau ma’aikatar hasashen yanayi ta gudanar da aikin harbin giza gizai a kalla sau 10 inda kusan da kyar ake ketara wuni ba tare da samun safkar ruwan sama ba a galibin jihohin wannan kasa lamarin da a fili ake ganin tasirinsa sakamakon yadda gonaki suka yi yabanya sosai hatta a yankunan da aka yi fama da fari a watan yulin da ya gabata.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Za A Yi Amfani Da Fasahar Zamani Wajen Samar Da Ruwan Sama