NIJAR: Yan Bindiga 11 Sun Ajiye Makamansu

Makamai Da 'Yan bindiga su ka mika

'Yan bindiga a Nijar na cigaba  da amsa kiran hukumomi kasar Nijar ta hanyar ajiye makamanai inda su ke fitowa suna rungumar shirin zaman lafiya.

'Yan bindiga 11 ne da suka addabi jama'a a iyakokin kasashen Libiya da Algeriya suka mika makamansu ga hukumomi. Makaman sun hada da harsasai masu yawa da kuma manyan bindigogi kirar AK47 da kuma kayakin yaki 'yan bindiga fiye da goma.

Sun mika makaman ne zuwa ga mahukuntan jihar Agadas bayan an ja shekaru masu yawa da matasan suka shiga wannan aiki a iyakokin kasashen Algeria da libiya da kuma Nijar tare da jefa jama’a cikin halin la’haula.

Bukin ajiye makamai 3

‘Yan bindigar sun ce sun amsa kiran da shugaban kasar Muhammed Bazoum, ya yi musu ne a kan su ajiye makamai tare da kawo karshe miyagun dabi’un da suka runguma.

Wadanda suka mika wuyar sun ce rashin aikin yi yasa suka shiga cikin wadannan ayyukan ta’addanci.

Hukumomi a Agadas dai sun yaba yadda yan bindigar ke ajiye makamai domin rungumar zaman lafiya tare da bada hadin kai ga jami’an tsaro.

Magaji Mamman Dada shi ne gwamnan jihar Agadas, ya kuma ce; "Zan isar da godiya ga wadannan yan bindigar da suka ajiye makamai don saboda zaman lafiya bayan kiran da shugaban Nijar ya yi. Kun san tsaro shi ne ginshikin cigaban kowace kasa. Muna kira ga sauran yan bindigar da ke rike da makamai da su zo su ajiye su domin rungumar zaman lafiya"

Mohamed Abubakar daya daga cikin 'yan kungiyar farar hula a Agadas na ganin wannan yunkurin na neman zaman lafiya abu ne mai kyau. To saidai ya kyautu a sanya ido akan tubabbu yan bindigar.

Yan bindigar sun dauki matakin dakatar da aikin na su ne domin acewar su karbar tayin zaman lafiya da shugaban kasar Nijar ya yi musu da kuma wasu dalillai na daban.

Saurari rahoton Hamid Mahmud:

Your browser doesn’t support HTML5

NIJAR: Yan Bindiga 11 Sun Ajiye Makamansu