Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Boko Haram 40 Sun Mika Wuya A Jihar Diffa


Mayakan Boko Haram Da Suka Mika Wuya
Mayakan Boko Haram Da Suka Mika Wuya

Kimanin mayakan Bokon Haram 40 ne suka mika wuya ga hukumomin jihar Diffa a Jamhuriyyar Nijar a wani mataki na karba kiran hukumomin jihar na ganin mayakan na boko haram sun mika wuya domin samun kulawa ta musamman a wata cibiyar gyara halinka dake garin.

DIFFA, NIGER - Gudumariya a cikin jihar ta Diffa, kawo yanzu dai mayakan Boko Haram kimanin dari shida ne suka mika wuya ga hukumonin jihar ta Diffa tun bayan kafa wannan cibiyar,daga jihar ta Diffa ga Aboukar Issa da karin bayani a wannan rahoton.

A cikin dai mayakan na boko haram 40 da suka mika wuya akwai mata 13 da kuma kananan yara 16, an kuma gudanar da bikin karabarsu ne a garin Geskeru dake da tazarar nisan kilometa 35 a gabas maso kudancin birnin Diffa.

Wani kwamiti na musamman da hukumomin jihar Diffa suka kafa domin karba tubabbin ‘yan boko haram shine ya karbi wadannan mayakan na Boko Haram.

A dai cikin shekarar 2017 ne hukumomin jamhuriyyar Nijar suka yi kira ga mayakan na boko haram na ganin mika wuya domin a kula da su a wata cibiyar gyara halika dake garin Gudumariya a cikin jihar ta Diffa,kawo yanzu dai mayakan na boko haram kimanin dari shida ne suka amsa wannan kira na hukumomin Nijar, to sai tubabbin ‘yan boko haram din sun yi kira ga hukumomin na Nijar na ganin sun kara daukar matakan kyautata masu rayuwa.

Humomin jihar ta Diffa sun bayyana cewa, har yanzu kofarsu na bude domin ci gaba da karbar ‘yan boko haram din dake bukatar tuba.

XS
SM
MD
LG