Yanzu haka ana cikin zullumi da juyayi mai tsananin gaske a cikin jahar Tahoua da ma daukacin jamhuriyar Nijar, inda wadansu mutane a kan babura su ka ketaro daga kasar Mali suka abka wa wadansu garuruwa 2 a cikin gundumar Tilliya da ke arewacin jihar Tahoua, wadda dama ke karkasin dokar tabaci a iyaka da Mali, inda mutane wajen 54 su ka hallaka, duk da yake a hukumance ana jiran gwamnatin kasar ta yi bayani game da lamarin.
Wannan al'amarin na zuwa ne, kwanaki kalilan bayan irin hakan ta faru a yankin Bani-Bangu a cikin jihar Tillabery, abinda ke sawa 'yan kasar cewa, gwamnati ta kara azama a kan iyakokin kasar da Mali, ganin ana toshe wani bangare kuma ruwa na bulla wani sashen.
Tuni dai bataliyar askarawan kasar ta isa wadannan garuruwa, ko da yake yunkurin jin ta bakin Magajin Garin Tilliya da shugaban wannan gundumar ya hadu da cikas, wani dan jarida mai fashin baki kuma dan yankin, Sidi Mohamed, ya yi karin haske kan abin da ya faru da kuma halin da ake ciki, ya na mai tabbatar da cewa sojojin sun kai dauki amma bayan aukuwar al'amarin.
Ga wakilin Muryar Amurka Harouna Mamane Bako da rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5