- Shine shugaban kasar Tanzania na biyar. Ya gaji jakaya Kikwete wanda ya yi mulki a kasar na tsawon shekaru goma- wa’adin mulki biyu.
- Ya zabi macen farko Samia Suluhu a matsayin mataimakiyar shugaban kasa, wadda a yanzu haka ta ke zaman shugaban kasa ta riko kafin rantsar da ita a matsayn shugaban kasa bisa tsarin mulkin kasa.
- Ya yi ilimi mai zurfi a fannin kimiyya, ya na da kwarewa a fannin ilimin sinadarai fannin da ya sami digirin digirgir. Ya yi karatunsa da rayuwarsa duka a kasar Tanzaniya.
- Ya wakilci mazabun Biharamulo ta gabas da Chato a majalisar dokokin tarayyar kasar daga inda ya tsaya takarar shugaban kasa.
- Ya yi minista na tsawon shekaru da dama a ma’aikatu dabam dabam.
- Yana daya daga cikin fitattun mutane a nahiyar Afrika da basu yarda da batun cutar Korona ba. Ya kuma ta musanta cewa akwai cutar a kasar sai bayan da wani babban sakatarensa ya mutu sakamakon kamuwa da cutar. Ya bayyana cutar Korona a matsayin :kwayar cutar ibilis da ba ta iya zama a jikin Almasihu”.
- An daina ganin shi a bainin jama’a tun ranar 27 ga watan Fabrairu, abinda ya sa aka yi ta rade radin cewa bashi da lafiya, batun da gwamnatin kasar ta musanta har da kama wadanda ake zargi da yayata labaran kage. Ba a sanar da rashin lafiyarsa ba sai bayan mutuwarsa.
- Da farkon mulkinsa an yi ta yaba kokarinsa na yaki da cin hanci da rashawa da bunkasa harkokin tattalin arziki abinda ya sa aka bashi lakabi “Bulldozer” amma daga baya aka fara zargin shi da bita da kullin siyasa.
- Gwamnatinsa ta rufe kafofin watsa labarai da dama, ta rika toshe hanyoyin sadarwar internet na ‘yan siyasa, da kuma kuntatawa ‘yan hamayya
- Ya mutu yana da shekaru 61 a duniya, yana shekarar farko a wa’adin mulkinsa na biyu. Ya rasu ya bar matarsa Janeth da ‘ya’ya biyu.
shugaban-tanzania-john-magufuli-ya-mutu
voa60-afirka-shugaba-john-magfuli-na-tanzania-ya-kalubalanci-sahihancin-wasu-magungunan-rigakafin
shugaban-tanzania-na-tababa-kan-ingancin-rigakafin-coronavirus
Karin bayani akan: Samia Suluhu Hassan, John Magufuli, da Tanzania.