Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kai wa Gwamnan Benue Samuel Ortom Hari


Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom.
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom.

"Sai da na yi gudun sama da kilomita daya da rabi ba tare da na tsaya ba. Ina godiya ga Allah da ya ba ni wannan karfi.” In ji Ortom.

Gwamnan jihar Benue da ke tsakiyar arewacin Najeriya Samuel Ortom ya sha da kyar bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai masa hari a lokacin da yake rangadin gonarsa da ke hanyar Gboko.

Wata sanarwa da shafin Twitter na gwamnatin jihar ya fitar, ta ce ‘yan bindigar da suka kai harin makiyaya ne.

Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari​, jihar Benue, Samuel Ortom, Nigeria, da Najeriya.

“Dazu nan tsagerun makiyaya suka kai hari kan tawagar Gwamna Samuel Ortom a hanyar Tyo-mu zuwa Makurdi – Gboko.” Sanarwar ta ce.

Wani bidiyo da gidan talbijin na Channels ya wallafa a shafinsa na yanar gizon, ya nuna Ortom yana yi wa manema labarai karin haske kan wannan hari da aka kai masa a ranar Asabar.

“A matsayina na manomi, na kan je rangadi gonata a hanyar Gboko. Akan hanyarmu ta dawowa sai muka fara jin harbe-harben bindiga, sai muka ga wasu mutane sanye da bakaken kaya, kuma ga dukkan alamau tsagerun Fulani ne.” In ji Ortom.

Gwamnan ya yaba da irin jarumatakar da masu tsaron lafiyarsa suka nuna wajen kare shi yayin da yake zargin kungiyar Fulani ta Miyetti Allah da kitsa wannan hari yana mai cewa zai shigar da su kara.

Kungiyar ta Miyetti Allah ba ta mayar da martani kan wannan zargi ba kuma yunkurin jin ta bakin shugabanninta ya cutura.

“Na gode Allah ina cikin koshin lafiya, saboda sai da na yi gudun sama da kilomita daya da rabi ba tare da na tsaya ba. Ina godiya ga Allah da ya ba ni wannan karfi.” Ortom ya fada a cikin bidiyon sanye da wata riga mai gajeran hannu, wacce wuyanta ya jike da alama ta zufa.

Ortom ya kara da cewa, idan ba zai iya zuwa gona ba a matsayinsa na gwamna da ke zagaye da jami’an tsaro, “waye zai iya zuwa? Wannan yana nuna irin halin kakanikayi da al’umar jihar Benue ke ciki.”

Fulani masu garkuwa da mutane
Fulani masu garkuwa da mutane

Cikin jawabin bidiyon, gwamna ya kuma yaba da matakin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari​ ya dauka na ba da umurni a harbe duk wanda aka gani da bindiga kirar AK47, sai dai ya nuna takaicin cewa, har yanzu bai ga jami’an tsaro sun fara daukan wannan mataki ba.

Matsalolin hare-haren ‘yan bindiga da sace mutane don neman kudin fansa a arewacin Najeriya sun zama ruwan dare, wadanda ake yawan alakantawa da Fulani makiyaya.

XS
SM
MD
LG