Kotun tsarin mulki Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da Bazoum Mohamed na jam'iyyar PNDS mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi.
A ranar 21 ga watan Fabrairu aka yi zaben a zagaye na biyu inda Bazoum ya samu kashi 55.66 daga cikin kashi 100 na kuri'un da aka kada, yayin da Mahamane Ousmane na RDR Tcandji ya samu kashi 44.34.
Kotun, wacce ta zauna a yammacin ranar Lahadi 21 ga watan Maris, ta ce Bazoum zai karbi ragamar mulki daga ranar 2 ga watan Afrilu domin fara wa’adinsa na shekara biyar.
Hakan na nufin wa’adin shugaba mai barin gado Mahamadou Issouhou zai kare kenan a ranar bayan kammala wa’adinsa na biyu na shekara biyar-biyar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Su dai bangaren ‘yan adawan sun yi watsi da sakamakon zaben suna kuma kalubalantar sa.
Lamarin har ya kai ga magoya bayan 'yan adawa gudanar zanga zangar nuna adawa da sakamakon zaben a wasu sassan kasar musamman a Yamai, babban Birnin kasar.
Hakan ya kai ga kama wasu daga cikin shugabannin bangaren adawa, wadanda ake zargi da tunzura jama'a su yi bore, zargin da suka musanta.
Kotun tsarin mulkin kasar, ita take da hurumin ayyana sakamakon zabe a mataki na karshe, duk da cewa hukumar zabe ta CENI, ta fitar da alkaluman da suka nuna dan takarar da ya lashe zaben a baya.