Mummunar fassarar da aka yi wa wani bidiyon da aka yada a kafafen sada zumunta, ita ce ta harzuka ‘yan Cote d’Ivoire suka shiga farautar ‘yan Nijar mazauna wannan kasa da nufin huce takaicin abin da suka kira wulakancin da jami’an tsaron Nijar suka yi wa ‘yan Cote d’voire akan hanyarsu ta zuwa cirani.
Shugaban kungiyar ONG JIMED mai kare hakkin ‘yan cirani Hamidou Manou Nabara na kallon abin a matsayin illolin da jahilci ke janyowa zamanktakewar al’umna.
A sanarwar da ta fitar gwamnatin Nijar ta yi cikekken bayani a game da abubuwan da suka faru da ‘yan kasar mazauna Cote d’ivoire bayan da shugaban kasa Mohamed Bazoum ya umurci ministan cikin gida da karamin ministan harakokin waje su tafi birnin Abidjan duba ‘yan kasar.
Gwamnatin ta dauki matakan gaugawa da nufin kaucewa sake faruwar irin wannan al’amari da ya janyo asarar dimbin dukiya.
Sakamakon damuwa da abinda ya faru a birnin Abidjan Kungiyar ‘yanCote d’ivoire mazauna Nijar ta kai ziyara a ofishin ministan harakokin waje domin jaddada goyon bayanta ga ‘yan Nijar mazauna Cote d’ivoire tare da jajantawa al’umma gaba daya.
Kwarariya a sha’anin amfani da kafafen sada zumunta Soueba Ibrahim na cewa tashin hankalin da ya biyo bayan yada labaran bogi wani abu ne da ya kamata ya zamewa al’umomi da gwamnatoci darasi.
Bayanai sun yi nuni da cewa bidiyon da ta haddasa wannan rudani an nade ta yau shekaru 2 da suka gabata bayan da jami’an tsaron Najeriya suka kama wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne.
Sake yada wannan bidiyo a farkon makon nan ya sa wasu ‘yan Cote d’ivoire tunanin ‘yan uwansu ne ke shan azaba a hannun jami’an tsaron Nijar. Rahotanni sun ce tuni hukumomin Cote d’ivoire suka kama wata mata da ake zargi da aikata wannan ta’asa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5