Mako daya bayan harin ta’addancin da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 71 a barikin Inates, Dakarun tsaron Jamhuriyar Nijer sun yi fareti a jiya laraba 18 ga watan disamba, a garin Tilaberi inda shugaba Issouhou Mahamadou da wasu takwarorinsa na yammacin Afrika suka halarta domin bukuwan ranar cika shekaru 61 da Nijer ta zama Jamhuriya.
An shafe sama da sa'oi 3 jami’an tsaro da jami’an fararen hula na fareti a gaban dubban mutanen da suka hallara.
Da ga cikin shugabannin kasashen Afrika da suka samu halartar taron, akwai shugaban kasar Ghana, Nanna Akufo Addo da shugaban kasar Burkina Faso, tare da shugaban rikon G5 Sahel, Roch Mark Christian Kabore, domin taya shugaba Issouhou Mahamadou murnar zagayowar wannan rana.
Faretin ya gudana ne a lokacin da ‘yan Nijer ke ci gaba da juyayin rasuwar wasu sojojin kasar kimanin 71 sanadiyar harin ta’addanci.
Bikin ya gudana ba tare da wata hatsaniya ba a sakamkon tsauraran matakan tsaron da aka dauka a bisa la’akari da matsananciyar matsalar tsaron da yankin na Tilabery ke fama da shi, sanadiyar halin da ake ciki a kasashen Mali da Burkina Faso.
Yankin Diffa dake fama da matsalar Boko Haram zai karbi bakuncin bukin Jamhuriya ta badi a karkashin tsarin da aka kira Diffa Ngla.
Saurari cikakken rahoton Wakilin muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5