Shugaban Jamhuriyar Nijar Issouhou Mahamadou, ya yi kashedi ga masu kiraye kirayen cewa kasar Faransa ta kwashe sojojinta daga yankin Sahel saboda zarginta da hada baki da ‘yan ta’addan arewacin kasar Mali.
A wajen wani taro na kungiyar G5 Sahel a birnin Yamai ne Shugaban ya bayyana haka, abinda ya sa wasu ‘yan kasar shiga maida mabanbantan ra'ayoyi da martani.
A lokacin taron, shugaba Issouhou ya bayyana cewa sukar lamirin masu tallafa wa kasashen Sahel a yakin da su ka kaddamar kan ‘yan ta’adda tamkar yada manufofin kungiyoyin ta’addanci ne da gangan ko cikin rashin sani.
To Sai dai tuni masu amfani da kafafen sada zumunta suka yi wa furucin shugaban ca, domin a tunaninsu bai dace irin wadannan kalamai su fito daga bakin wani mai rike da mukami makamancin na sa ba. Shugaban jam’iyyar adawa ta MDN, Annabo Soumaila na da irin wannan ra’ayi.
Matsin lambar da ‘yan kasashen yankin Sahel ke yiwa kasar Faransa a ‘yan kwanakin nan don ganin ta kwashe sojojinta daga wannan yanki wani yunkuri ne da za a iya cewa ya janyo bambancin ra’ayi a tsakanin hukumomi da talakawansu. Kalla Hankourao, Ministan harkokin wajen Nijer, ya ce Nijer ce ta gayyato dakarun don su yi yaki da ‘yan ta’adda saboda sun san cewa yakin ba karamin abu ba ne.
A ra’ayin Abdou Elhadji Idi, na kungiyar kare hakkin jama’a ta FSCN, kalaman shugaba Issouhou akan masu sukar Faransa wani abu ne da aka yi da nufin faranta ran Emmanuel Macron wanda a makon jiya ya nuna fusata akan yadda aka dora wa kasarsa tsana a yankin Sahel.
Harin da ya lakume rayukan gomman sojoji a makon jiya a barikin sojan Inates da ke iyakar Nijar da Mali shi ne ya sake farfado da muhawara game da rawar da Faransa ke takawa a yaki da ‘yan ta’adda ganin yadda rundunar sojan Barkhane ke bai wa ‘yan tawaye kariya a karkarar Kidal.
A saurari cikakken rahoton acikin sauti daga wakilinmu a Yamai Souley Barma:
Facebook Forum