A yayin da take bukin cika shekaru hudu da kafuwa, jam’iyar Adawa ta MPN Kishin Kasa ta yi bukin rantsar da tsohon ministan harkokin wajen jamhuriyar Nijar Ibrahim Yakouba, a matsayin dan takarar da zai tsaya mata a zaben shugaban kasa na 2020.
Dubban magoya bayan MPN Kishin Kasa da suka fito ciki da wajen jamhuriyar Nijar ne suka halarci gangamin da uwar jam’iyar ta shirya a dakin taro na Palais Du 29 Juillet, dake birnin Yamai, domin jaddada goyon baya ga shugabanta Ibrahim Yakouba.
Tuni magoya bayan wannan jam’iya suka fara jan damara don ganin nasu dan takarar ya samu cin nasara a zaben badi, kamar yadda shugabar matan kishin kasa Hajiya Baraka Sabo ta bayyana.
Jam’iyar MPN Kishin Kasa mai manufofin hada kan kasahen Afrika, ta gayyaci ‘yan siyasa daga kasashe da dama na nahiyar domin halartar shagulgulan wannan buki wanda ta wani bangare ke da matsayin murnar cika shekaru hudu da kafuwarta.
A karshen shekarar 2015 ne Ibrahim Yakouba da wasu abokansa suka kafa jam’iyar MPN Kishin Kasa, bayan da jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki ta dakatar da shi daga sahun ‘ya yan ta.
Jam’iyar wacce a yau ke adawa da gwamnatin Renaissance na da kujerun wakilci a Majalisar Dokokin kasa, abin da ya sa magoya bayanta ke ganin za su bada mamaki a zabubukan 2020 da 2021.
Ga rahoto cikin sauti.
Facebook Forum