Abin da suka ayyana a matsayin babban cigaba a kokarin samar da dunkulalliyar kasar Mali bayan shafe shekaru da dama na fama da aika aikar ‘yan ta’adda da wadanda suka daure masu gindi.
Ta hanyar sanarwar da aka aike wa manema labarai wace kakakin majalissar CNSP Colonel Major Amadou Abdourahamane ya karanta hukumomin mulkin sojan Nijer da gwamnatin rikon kwaryar kasar suka bayyana farin cikinsu game da nasarorin da sojojin FAMA na kasar Mali suka samu a yayin kafsawar da ta basu damar sake kwato garin Kidal na arewacin kasar daga hannun ‘yan ta’adda.
Yace wannan gari da aka yi wa kawanya a baya ya kasance a karkashin ikon ‘yan ta’adda da wadanda suka daure masu gindi masu alhalin haddasa tashin hankali a Mali da ma yankin sahel baki daya a tsawon shekaru da dama. majalissar CNSP da gwamnati na jinjina wa sojojin FAMA da al’ummar Kidal masu diyauci da ma al’ummar Mali baki daya da suka dage da jimiri wadanda a karshe suka bada damar ceto wannan gari.
Ba yau ba masana sha’anin tsaro ke gargadi akan bukatar kwato garin kidal daga hannun ‘yan bindiga kasancewarsa cibiyar kungiyoyin ta’addancin da suka saje da na ‘yan tawayen arewacin Mali saboda haka ake ganin wannan galaba ta sojojin kasar abin alfahari ne inji Ibrahim Moussa shugabn kungiyar ‘yan jarida masu kula da sha’anin tsaro da zaman lafiya RJPS, koda yake sabon yanayin da aka shiga abu ne da ke wajbata wa kasashe makwaftan Mali su tsaurara matakan riga kafi.
Garin Kidal da ke a km 1540 da Bamako babban birnin Mali na gab da iyakokin kasashen Nijer da Aljeriya, ya fada hannun ‘yan tawaye a shekarar 2014 lamarin da ake dangantawa da bazuwar makamai bayan faduwar gwamnatin Kaddafi na Libya.
Tun daga wancan lokaci shiga garin ya yi wa sojojin Mali wuya saboda yadda kungiyoyin ‘yan tawaye ke ayyana shi a matsayin matsirar kwatar ‘yancin kan yankin Azawad kuma alakar da ake zargin sun kulla da dakarun da Faransa ta girke a yankin ya sa a ke daukan abin tamkar wata shiryayyiya. Mafari kenan hukumomin mulkin sojan Mali da abokan huldarsu na Wagner suka kadammar da samamen kan garin Kidal bayan ficewar sojojin Faransa da na Minusma daga Mali.
Saurari rahoton Sule Barma:
Your browser doesn’t support HTML5