Nijar ta Koka Kan Matsalolin Tsaro Kan Al'umarta Dake Kan Iyaka da Nigeria

Shugaban Nijar Muhammadu Isouffe.

Magajin garin Dan Isa dake kan iyakar Nijar da Najeriya ya gayawa Sashen Hausa cewa 'yan binidga daga Najeriya suna barzana ga jama'ar da suke kan yankin.

Mazauna yankin sun koka kan barazanar da suke fuskanta daga mutane da suka kira 'yan fashi da makami daga Najeriya, wadanda suke tsallakawa suzo suyi barna sannan su koma.

Magajin garin Dan Isa, Mallam Hamza Garba, wanda ya zanta da Shu'aibu Mani, yace a baya bayan nan, 'yan fashi da makaman sunzo garin suka tasamma wani gida, Allah cikin ikonsa karen mai gidan ya fara haushi, dalilinda ya samu ya tsere, amma 'yan binidgar suka kutsa cikin gidansa suka kama 'yarsa 'yar shekara 14 da haifuwa. Amma aka ceto ta daga baya.

Da jami'an tsaro suka fara sintiri a yankin, sai 'yan fashin suka kaura suka koma yankin da babu jami'an tsaro. A wani hari da suka kai kan rugar fulani, sun kame matan fulanin suka tafi dasu, kuma har yanzu ba'a san inda matan suke ba.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar ta koka kan batun tsaroa a kan iyakarta da Najeriya