'Yan sandan Niamey, babban birnin kasar jamahuriyar Nijer sun kara tsunduma cikin wani yajin aiki da bore a karo na biyu a jere cikin watanni biyu, wato watan jiya na Oktoba da kuma wannan wata na Nuwamba.
Yajin aikin da boren na da nasaba ne da rashin biyan su albashi, da rashin wadatar kayan aiki da kuma wasu bukatun da suka gabatar da nufin neman kyautatuwar aikin su da inganta rayuwar su.
'Yan sandan su dakatar da aiki na tsawon kwanaki biyu, duk da cewa sun bayyana a wuraren ayyukan su amma ba cikin kayan sarki ba, illahirin 'yan sandan na cikin farin kaya.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a birnin Niamey Abdoulaye Mamane Amadou ne ya aiko da rahoton: