Wasu kwararru daga yankuna daban-daban na kasar Jamahuriyar Nijer na gudanar da wani taron binciko dalilan dake haifar da fitintinu da tashe-tashen hankula tsakanin al'ummar kasar domin a samar da hanyar magance su.
Hukumar raya karkara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNDP, da Hukumar Koli mai Fafutukar Dawwamar da Zaman Lafiya a Nijer ne suka hada guiwa su na gudanar da taron da nufin tsara wani kundin da hukumomin kasar Nijer zasu yi amfani da shi su yi rigakafin afkuwar rigingimu a kasar, musamman ma idan aka yi la'akari da cewa kasar ta Nijer na zagaye da kasashen dake fama da karancin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Wakilin Sashen Hausa a birnin Niamey Abdoulaye Mamamne Amadou ne ya hada rahoton kuma ya aiko.