Gwamnan yankin Issoufou Mamane ya shaida wa gidan talabijin na jama'a da yammacin Laraba cewa, "bayan kwanaki da dama da ake ta bin sa, a karshe mutanen mu sun kama shahararren (Kachalla) Baleri da wasu mutanensa."
Tashar talabijin ta bayyana wasu faifan bidiyo na wasu mutane goma sha biyu da aka daure da sarka da fuskar su a rufe suna zaune a kasa, ta na mai cewa an kama su yayin wani taron su inda su ke shirya kai hare-hare kan jami'an tsaro".
Gwamnan yankin Maradi ya ce Baleri daga jihar Zamfarar Najeriya yana lamba 40 a jerin sunayen sojojin Najeriya da ake nema ruwa a jallo.
A cewar gidan talabijin na jama'a, Baleri ya shiga cikin "hare-hare da dama inda aka zubar da jini a Najeriya", da kuma harin da aka kai a ranar 22 ga watan Fabrairu da ta gabata wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Nijar hudu daga bangaren yaki da ta'addanci da suka kama shi a ranar Laraba.
“Masu fyade ne, barayin shanu da kuma masu kashe mutane ba imani,” in ji mai shigar da kara na babbar kotun Maradi, Adam Adamou.
Dakarun sojojin kasashen biyu sun gudanar da ayyukan hadin gwiwa domin dakile tashe tashen hankula.
Sama da shekaru 10 dai, iyakar Najeriya da Nijar ta kasance maboyar kungiyoyin ‘yan bindiga wadanda ke sace fararen hula domin neman kudin fansa da kuma satar shanu.
~ AFP