Ministan Tsaron Najeriya, kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar a hirarsa ta musamman da Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha, ya tabo batuttuwa da dama game da tsaro musamman a arewancin Najeriya.
Badaru ya ce tun ya fara aiki, ya gana da dukkan manyan tsoffin sojoji da ma’aikatan tsaro, ciki harda tsohon Shugaban mulkin sojin Najeriya, Abdulsalam Abubakar, don samun shawarwarin magance matsalar tsaro.
Ya kuma nanata cewa babban matsalar tsaro shine rashin haddin kan shuwagabannin tsaro, amma ya zuwa yanzu, an samu haddin kai a tsakanin shuwagabannin na tsaro da suka hadda da ‘yan sanda da jami’an fararen hula wanda shine tushen nasarorin da ake ta samu.
Ya kara da cewa cikin shekara dayan da aka cika, an samu nasarar kashe ‘yan ta’adda da barayin daji kusan 9,800, an kuma kama kimanin 'yan bindiga 7,000, sannan kuma an kwato mutanen da aka sace kusan 4,700.
Badaru ya ce babban matsalar da su ke fuskanta shine na samun haddin kan jama’a wajen bada ingantaccen bayanai.
Saurari cikakken hirar a sauti:
Dandalin Mu Tattauna