NIAMEY, NIGER - Wasu kuma na ganin wannan mataki tamkar wani abin da ka iya rufe hanyoyin samun kaudaden shiga daga waje a dai dai lokacin da kasar ke neman mafita kan takunkumin kungiyar ECOWAS.
A wasikar da ya tura wa shugabanin ma’aikatar shige da ficen kaya bisa umurnin da aka bayar daga ofishin ministan kudin kasar, shugaban hukumar Douane ta kasa Kanal Abou Oubandawaki, ya umurci jami’ansa su hana fitar da iskar gas daga Nijar har sai yadda hali ya yi, amma kuma ba tare da fayyace dalilan daukan wannan mataki ba.
Bayanai sun yi nuni da cewa sau tari iskar gas din da aka ware don amfanin cikin gida kan tsallaka zuwa kasuwanin kasashen ketare ta barauniyar hanya dalili kenan da shugaban kungiyar kare hakkin jama’a a fannin makamashi ADDC WADATA, Malan Maman Nouri yake ganin matakin mahukuntan dubara ce ta toshe hanyoyin fasakwabri.
Sai dai kuma a wani bangare za ta yiwu wannan abu ne da ke neman maida martani ga kasashen da suka yi ruwa da tsaki wajen ganin CEDEAO ta kakaba wa Nijar takunkumi a washe garin juyin mulkin 26 ga watan yuli.
Shi ma shugaban kungiyar kulawa da rayuwa Hamidou Sidi Fody, ya nuna gamsuwa kan wannan mataki da ya ayyana a matsayin na kare darajar kasa, koda yake kuma a cewarsa akwai wani hanzari ba gudu ba.
A shekarar 2012 ne Nijar ta fara hako iskar gas dinta, wato shekara daya bayan soma ayyukan hakar man fetur daga rijiyoyin mai na Agadem da ke jihar Diffa.
Alkaluma sun yi nuni da cewa kasar ta hako tonne 60,000 na iskar gas a shekarar 2020 wanda kuma a kan yi amfani da shi a matsayin makamashin girke-girken abinci kafin daga bisani a fara fitar da shi zuwa kasashe makwafta kamar Najeriya da jamhuriyar Benin.
A bisa al’ada hukumomin kasar kan dakatar da ayyukan matatar SORAZ da ke Zinder a tsakanin watanni biyu na karshen shekara don gudanar da ayukan gyare-gyare abin da ya sa wasu ‘yan kasa ke ganin watakila matakan riga kafin da aka saba dauka ne idan irin wannan lokaci ya zagayo don kaucewa tsinkewar iskar gas a nan cikin gida.
Saurari açıkken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5