BIRNIN N’KONNI, NIGER - Tun lokacin da ya yi wa ‘yan kasa jawabi ne a watan jiya, Shugaban Majalisar koli ta soja da ta karbe mulki daga Mohamed Bazoum, Janaral Birgediya Abdurahamane Tchani, ya bada sanarwar girka babbar mahawara tsakanin ‘yan kasa, domin kayyade lokaci da ma yanayin da ya kamata su gudanar da rikon kwarya, da kuma wane irin kundin tsarin mulki Nijar zata bullo da shi.
Tuni dai aka soma wadannan mahawarori ta hanyar komitoci dake kumshe da kungiyoyin fararen hulla, da na ma'aikata da ‘yan siyasa da na mata da matasa, da manoma da makiyaya da sauran su, a matakai na kananan hukumomi, gundumomi da kuma jahohi, inda daga bisani za'a hada a
Daya daga cikin ababen da suka sha kawo cikas ga tafiyar siyasa a Jamhuriyar Nijar, shine rashin cika alkawari da bin doka game da kason da ya kamata a kebewa mata a mukamai na siyasa da na aikin bariki.
Wannan mahawarorin na dai gudana yanzu haka a dukkan kananan hukumomi 266, da gundumomi 63 da jahohi 8 na Jamhuriyar Nijar wanda zai share fage ga babban taro na kasa da zai yi shinfida ga shatawa kasar sabon kundin tsarin mulki.
‘Yan kasar Nijar na zura idanu ne, domin ganin ko a wace alkibla ce, mahawarorin nan za su karkata kasar a nan gaba, a daidai lokacin da ake ci gaba da yin addu'o'i a ko'ina a cikin kasar domin samun saukin halin da ta samu kanta a ciki.
Saurari cikakken rahoton Haruna Mamman Bako:
Dandalin Mu Tattauna