Nijar Ta Dauki Matakin Hana Fitar Da Hatsi Zuwa Ketare

Wasu 'Yan Kasuwa Na Auna Shinkafa

A yayinda aka fara girbe amfanin gona a yankuna da dama na jamhriyar Nijar ofishin ministan kasuwanci ya hana fitar da abincin da suka hada da shinkafa da hatsi da dawa zuwa ketare da nufin samar da wadatar cimaka akan farashi mai rangwame a kasuwannin kasar.

Ganin yadda a irin wannan lokaci na kaka wasu ‘yan kasuwar kasashen waje da ma wasu a nan cikin gida ke saye amfanin gona da arha kuma su jibge don sayarwa a gaba da tsada ya sa gwamnatin Nijar kafa dokar hana fitar da abincin da suka hada da hatsi da shinkafa da dawa.

Shugaban kungiyar ADDC WADATA mai fafutikar kare hakkin masu saye don amfani Malan Maman Nouri na cewa abin na iya tasiri wajen wadatar da jama’a da cimaka ya kuma yi sanadin saukar farashi a kasuwanni.

Sai dai hukumomin sun ce matakin bai shafi sauran kasashen kungiyar AES ba wato Mali da Burkina Faso a bisa wasu dalilai.

Galibin jama’ar Nijar musamman mazauna karkara na dogara da noman damuna don tanadin cimaka, galibi dawa da hatsi da wake yayinda a wasu yankunan a kan kwatanta noman shinkafa.

La’akari da yadda canjin yanayi ya fara shafar sha’anin damuna ya sa hukumomi da kungiyoyin ci gaban al’umma kwadaitar da ‘yan kasar fa’idar maida hankali kan ayyukan noman rani musamman a shekarun da aka fuskanci gardamar damuna.

Sararım çıkakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar Ta Dauki Matakin Hana Fitar Da Kayan Amfanin Gona Don Wadata Kasar