Nijar Ta Ayyana Zaman Makoki Bayan Da Mahara Suka Kashe Sama Da Mutum 50

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ayyana zaman makokin kwanaki 3 daga da nufin nuna juyayi a game da rasuwar wasu ‘yan kasar sama da 50 da ‘yan bindiga suka yi wa kisan gilla a wasu kauyukan gundumar Banibangou ta jihar Tillabery.

Wannan mummunan al’amari da ya rutsa da fararen hula ya wakana ne a ranar Litinin din da ta gabata a yayin da mutanen suka fito daga cin kasuwar garin Banibangou akan hanyarsu ta komawa gida Chinagoder da Darey Dey.

Fataken wadanda ke cike a wasu motocin jigila 2 sun fada tarkon ‘yan bindigar da suka kafa shinge akan hanya inda suka dinga karkashe su guda guda kamar yadda kakakin gwamnatin Nijar Abdourahamane Zakaria ya bayyana a wata sanarwa.

Karin bayani akan: Nijar, Nigeria, da Najeriya.

Sanarwar ta ce akalla mutum 58 ne suka halaka sakamakon aika-aikar ta ‘yan bindigar da kawo yanzu ba a tantance ko su waye ba sannan sun kona motoci 2 da rumbuna da dama na cimaka kafin suka arce da motoci biyun.

A cewar gwamnatin ta Nijar, ta kara tsaurara matakan tsaro kuma tuni aka kaddamar da bincike domin gano wadanda suka tafka wannan ta’asa don ganin an gurfanar da su gaban kuliya.

Domin nuna juyayi akan wannan rashi hukumomin Nijar sun ayyana zaman makoki na kwanaki 3 a duk fadin kasar daga ranar Laraba 17 ga watan Maris inda za a sassauta tutocin kasar a tsawon wadanan kwanaki da nufin karrama wadannan mamata.

Wannan shi ne karo na 2 da ‘yan bindiga ke halaka fararen hula a yankin Tillabery a kasa da wata 3 domin ko a ranar 2 ga watan Janairu da ya gabata ‘yan bindiga sun halaka fararen hula kimanin 100 a kauyukan Zaroumdareye da Tchambangou da ke gundumar Ouallam a yankin Tilabery.

Hakan na faruwa ne duk kuwa yankin yana daga cikin yankunan da ke karkashin dokar ta-baci ga kuma sojojin gida da na waje da aka girke akan iyakokin kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso da sunan yaki da ta’addanci.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar Ta Ayyana Zaman Makoki Bayan Da Mahara Suka Kashe Sama Da Mutum 50