A taron manema labaran da suka kira a Yamai a dazu da hantsi, mambobin kwamitin tsare tsaren wannan babban taro sun fara ne da waywaye akan mawuyacin halin da matsalar tsaro ta jefa jama’a a jihohin Diffa Tahoua da Tilabery inda barayi da ‘yan ta’adda ke cin karensu ba babbaka, kuma a cewarsu jihar Tilabery ta fi ko ina dandana kuda sanadiyar lalacewar al’amura a kasar Mali.
Tsohon ministan raya al’adun Nijar, Alhaji Assoumana Malan Issa, mamba ne a wannan kwamiti.
Ya kuma ce tun 2015 Nijar ta fuskacin tashin hankali inda 'yan ta'dda suka addabi jihohin Tilabery, Tahoua da Diffa suka kuma kashe jama'a da dama suka kuma raunata wasu.
Lura da mawuyacin yanayin da ake ciki ne ya sa shugabanin al’umar ta Tilabery a karkashin jagorancin ministan cikin gida Hamma Souley Adamaou suka kudiri aniyar kiran babban taron da zai hada wakilai daga sassa daban-daban a ranakun Lahadi 13 da Litinin 14 ga watan Maris a Tilabery domin zakulo shawarwarin da za su ba da damar warware kullin da ya haddasa tsayawar harakoki a baki dayan jihar.
Jihar Tilabery mai dauke da kabilun da suka hada da Zabarmawa, Hausawa, Fulani, Bugaje da Gurmawa, yanki ne dake iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso.
Noma da kiwo da kamun kifi su ne manyan ayyukan da jama’a ke dagaro akansu, aika aikar ‘yan ta’addan dake ketarowa daga makwabta ta haifar da yawaitar ayyukan ‘yan bindiga yayin da sau tari dalilan kabilanci ko fadan manoma da makiyaya ke haddasa ramuwar gayya.
Lalacewar al’amuran tsaro ya sa gwamnatin Nijar kafa dokar ta baci a jihar lokaci guda da wasu jihohin dake cikin irin wannan yanayi, yayin da dakarun kasar ta Nijar da na wasu kasashe aminnai ke aikin sintiri dare da rana.
Sai dai abin na kama da tamkar ana magani kai ya na kaba inda dubban mutane suka tserewa garuruwansu .
Saurari cikakken rahoton cikin sauti :
Your browser doesn’t support HTML5