Almajirai da ‘yan mata masu aikatau da yaran dake gararamba, wani rukuni ne na al’uma da kusan ana iya cewa an manta da shi a wannan zamani na fama da annobar Coronavirus, mafarin shirya wannan taron horo na kungiyar kare hakkin yara CONAFE Niger don gwadawa likitoci dubarun kula da irin wadanan yara a ci gaba da karfafa matakan dakile yaduwar cutar ta COVID-19.
Kungiyar kasa da kasa mai kula da sha’anin bunkasa kiwon lafiya Medecin du Monde reshen kasar Belgium ce ke dauke da dawainiyar wannan taro wanda daga bisani mahalartansa ke da alhakin koyar da mambobin wasu kungiyoyi masu zaman kansu, dubarun da suka koya a yayin wannan zama.
Kuma la’akkari da hadarin da likitoci ke fuskanta a wannan lokaci na annoba, ya sa MDM Belgique kaddamar da wannan shiri da soma ba su horo kamar yadda wakilin kungiyar Boubacar Karadje ya bayyana.
A ranar Laraba 16 ga watan Yuni ake kammala wannan taro dake daidai da ranar yaran Afirka wacce ta samo asali daga kisan daruruwan yara bakar fatar da aka bindige a yayin zanga-zangar adawa da wariyar launi fata da ta gudana a 1976 a birnin Soweto na Afirka ta kudu.
Saboda haka shirya wannan taro a lokacin da ake tunawa da wadanan yara yunkuri ne da CONAFE Niger da MDM Beligique ke amfani da shi don tunatarwa game da ‘yancin yara a fannin kiwon lafiya.
Saurari Rahoto Cikin Sauti Daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5