Nijar Na Baya Wajen Samar Da Ababen More Rayuwa A Kasar - Rahoto

Duk da matakan da gwamnatin Nijar ta dauka a shekarun baya-bayan nan don ganin kasar ta samu ci gaba a  alkaluman kididigar da hukumar UNDP ke fitarwa a kowace shekara kan batun ci gaban rayuwar jama’a, da alama har yanzu tsugune bai kare ba.

Rahoton da hukumar UNDP ta fitar a makon jiya ya ayyana Jamhuriyar Nijar ta na baya a duniya wajen samar da ababen more rayuwa bayan gudanar da bincike a kasashe 189.

Alkaluman kididigar hukumar UNDP na matsayin wani ma’unin mizanin yanayin rayuwar da talakkawa ke ciki wanda a gefe daya ke zama wani matakin ta da gwamnatoci daga barci game da nauyin da ya rataya a wuyansu a matsayinsu na masu alhakin kyautata rayuwar ‘yan kasa.

Kamar yadda abin yake, a shekarun baya, rahoton na shekarar 2020 na cewa Nijar ce ta karshe a duniya wajen tanadin ababen bukatun dan adam, abin da ya sa shugabannin kungiyoyin kare hakkin jama’a irinsu Nassirou Saidou ke cewa, lokaci ya yi da za a a dauki matakan canza al’amura.

Rahoton wanda ke shafar ayyukan shudaddiyar gwamnatin tsohon shugaban kasa Issouhou Mahamado, na iya zamewa shugaba Mohamed Bazoum wata manuniyar hanyoyin da za su bada damar sauya al’amura a tsawon wa’adin mulkinsa.

Rashin gamsuwa da matsayin Nijar a rahoton na Majalisar Dinkin Dinkin mai kula da bunkasa karkara ya sa shugaba Issouhou Mahamadou a zamaninsa ya kafa wani kwamitin ministoci mai alhakin nazarin hanyoyin inganta matsayin kasar yayin da hukumar kididdiga ta kasa INS a na ta bangare ta shiga yunkurin inganta hanyoyin tattara bayanai.

Sai dai sabbin alkaluman da UNDP ta fitar a karshen mako na nunin har yanzu da sauran aiki.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar Na Baya Wajen Samar Da Ababen More Rayuwa A Kasar - Rahoto