Yayin da Jamhuriyar Nijar ke shirin gudanar da zabukanta na gama gari a farkon shekara mai zuwa, jam’iyyun kasar na ta kokari suga cewa sun fitar ‘yan takarar da za su tsaya a karkashin totocinsu a matakaia daban daban.
Yanzu haka magoya bayana jam’iyyar MPR ta Albadeh Abuba a Maradi, sun kammala taron tsaida ‘yan takararsu na jiha a zabukan da ke tafe.
Wannan dai ya zo wa mutane da dama da mamaki ganin cewar jam’iyyar jaririya ce da aka kafa a kwananan.
Bayan wannan taro da suka yi, wakilin Muryar Amurka, Chaibou Mani ya ji ta bakin, Minista Malam Salisu Adah da ke magan da yawun Albadeh, kan abubuwan da suka tsaida yayin da ake shirye shiryen zuwa gamgamin jam’iyyar baki daya.
Ga yadda hirar ta su ta kaya:
Your browser doesn’t support HTML5