NIJAR: Masu Fafutuka Sun Yi Tattaki Sakamakon Matsalolin Dumamar Yanayi

Kwararowar Hamada

Masu fufutukar kare muhalli sun yi tattaki a yau zuwa birnin Yamai na Nijar da nufin nuna rashin jin dadi game da abin da suka kira jan kafar da ake fuskanta wajen tilasta wa kasashen da ke gurbata muhalli biyan diyya sakamakon illolin da suke haddasawa al'umomi da muhalli a kasashe masu tasowa

Nijar dake tsakiyyar yankin Sahel na fama da kwararowar hamada da zaizayar kasa lamarin da ke haddasa tsaikon saukar ruwan damuna ko ambaliyar ruwa a wani zubin.

Masana sun kididdige cewa hektar 200,000 na kasar noma da kiwo ne ke gurabacewa a kowace shekara a jamhuriyar Nijar sakamakon canjin yanayi, matsalar da ke tattare da wasu tarin illolin da ke shafar muhalli.

Haka kuma abin ke haddasa asarar rayukan jama’a da na dukiyoyi yayin da dumamar yanayi ke janyo matsalolin lafiya a mutane.

‘Yan fafutika ne na gamayyar kungiyoyin kare muhalli da zanga-zangar lumana a birnin Yamai a wannan Alhamis 7 ga watan Nuwamban 2024.

Suna masu nuna rashin jin dadi kan yadda manyan kasashen duniya musamman masu arzikin masana’antu ke buris da shawarwarin da aka tsayar a taron kare muhalli na duniya na 2022 da 2023 a game da bukatar biyan diyya ga kasashen Afrika wadanda ba su ci kasuwa ba runfa ta fada kansu.

Kungiyoyin wadanda ke shirin halartar babban taron yanayi da muhalli na duniya da za a bude a ranar 11 ga watan Nuwamba a birnin Baku na Azerbaijan sun kudiri aniyar ci gaba da wannan gwagwarmaya ta neman yi wa kasashe masu tasowa adalci kamar yadda kakakin gamayyar RJNCC Issa Garba ya shanda wa Muryar Amurka.

Kasashen Sahel irin su Nijar na kan gaba a jerin mafi dandana kudar illolin canjin yanayi a duniya abin da masana suka ayyana cewa ya haifar da matsanancin talauci da karancin abinci sannan ana danganta lalacewar al’amuran tsaro a yankin da wannan matsala a wani lokacin da manyan kasashen duniya ke azurta kansu da ma’adanan wadanan kasashe.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

NIJAR: Masu Fafutuka Sun Yi Gangamin Yaki Akan Illolin Yanayi Da Ake Fuskanta A Afirka.MP3