Yau kasashen duniya ke bikin tunawa da ranar yaki da gusowar hamada wace majalisar dinkin duniya ta kebe domin tunatar shuwagabanin nauyin da ya rataya a wuyansu don kara jan damarar tunkarar wannan matsala dake ci gaba da barazana ga rayuwar halittu da tsirai da sauran albarkatu.
A bana taken yaki da kwararuwar Hamada, wace ta samo asali a 1994, “Shine mu kare duniyar mu ta hanyar aiyukan farfado da kasa” wanda hakan ke nufin irin babbar barazanar da Hamada ke yiwa kasashen duniya, ta la’akari da koma baya da matsalolin gusowar Hamada ke hadasawa kasashe masu tasowa a fanin aiyukan ci gaba irin su noma da kiwo da sauransu.
Malam Ila Kane, shugaban wata kungiyar kare muhalli, a Nijar yace gusowar Hamada na taimakawa wajen karfafa sauyi yanayi kuma ya kara da cewa Noma da kiwo, na fuskantar kalubale.
Masana sun bayana cewa matsalar Hamada, ta mamaye akalla kashi biyu daga cikin uku na fadin kasar Nijar abinda ke nuna matukar bukatar daukar matakan hadin guiwa da makwabtanta, sai dai akwai alamar saku saku daga bangaren magabata wurin daukar matakan da suka dace.
Minista kare muhali da samarda ci gaba mai durewa na jamhuriyar Nijar, Barmou Salifou, yace gwamnatin kasar ta Nijar, ta gudanar da dinbin aiyukan farfado da kasar Noma, a shekaru biyar din da suka gabata.