La’akari da yadda lokaci ya fara karatowa a wa’adin shekara daya da dokokin CEDEAO suka yi tanadi wa wadannan kasashe da suka sanar da ficewarsu daga sahun mambobinta ya sa gwamnatocin Mali, Nijar da Burkina Faso suka dukufa da neman hanyoyin maye guraben muhimman ababen dake da nasaba da kungiyar, don ci gaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika.
Mafari kenan ministocin cikin gidan kasashen uku suka yi zama a Bamako don neman mafita a kan batun takardun bulaguro.
Ministan cikin gidan Nijar Janar Mohamed Toumba ya ce dukkanmu mun yarda da samfarin fasfon Burkina Faso a matasyin mafi dacewa da kasashenmu haka kuma samfarin katin kasar Mali na iya zama mafi cancanta da yankin nan namu. Kuma hakan ya yi daidai domin idan aka lura za a gane cewa abin zai fi zuwa mana da sauki.
Mamba a kungiyar farar hula ta MPCR Ibrahim Namema ya yaba da matakin domin a cewarsa abu ne da zai karfafa cudanya a tsakanin al’umomin kasashen AES.
Ministan ya kara da cewa idan komai na tafiya kamar yadda aka tsara za a fitar da wadanan takardu a shekarar 2025.
Kuma bayan ganawa da shugaban rikon kungiyar shugaban gwamnatin Mali Janar Asimi Goita, ya ce mataki na gaba shine a hanzarta daukan matakan isar da su hannun jama’a.
Da yake bayyana ra’ayinsa a kan wannan yunkuri, Sahanine Mahamadou wani mai hamayya da gwamnatin mulkin sojan Nijar na ganin abin a matsayin wanda ka iya haddasa cikas ga harkokin ‘yan Nijar mazauna ketare.
A jajibirin cika shekara daya da kafa kawancen AES ne shugaban rikon kungiyar Assimi Goita na Mali ya sanar cewa Nijar da Mali da Burkina Faso za su bullo da sabon fasfo, nan ba da jimawa ba domin jama’ar yanki.
A ranar 28 ga watan Janairun 2024 kasashen uku suka sanar cewa sun fice daga CEDEAO saboda zargin kaucewa ainihin manufofin da aka kafata, wanda yazuwa yanzu yunkurin mayar da su sahun dangi ya faskara.
A ci gaba da sauke shingayen kasashen uku a taron da suka yi a tsakiyar makon jiya a birnin Yamai sun cimma wata yarjejeniyar sassauta farashin wayar tarho a tsakananinsu.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5