Kungiyar ta shirya muhawarar ne da nufin bullo da shawarwarin da zasu taimaka a samo mafitar matsalolin da ake fuskanta a fannoni daban daban.
Taron ya maida hankali a kan shugabanci da irin nauyin da ya rataya a wuyan ma’ikanta da talakawa a Nijer. Maudu’in da aka baje a kan teburin ya hada kan dan majalissar dokokin kasa jigo a jam’iyar PNDS mai mulki honorable Kalla Moutari da babban magatakardan madugar jam’iyun hamayya Moden Lumana Maman Sani Malan a tsakiyarsu masanin dokokin tsarin mulki Dr Boubacar Amadou Hassan a albarkacin wannan mahawwara da AEC ta shirya don neman mafitar matsalolin dake maida hannun agogo baya a sha’anin ci gaban wanann kasa.
Awoyi a kalla 2 aka shafe ana sauraren bahasi daga shika shikan wannan mahawara tare da amsa tambayoyin wadanda suka hallara da nufin daukan darasi. Matashi dan siyasa daga jam’iyar MPN Kishin kasa Yahaya salifou Mohamed ya ce ya sami karuwa daga bayanan da ya ji a yayin wannan haduwa.
Haka shi ma Boubacar Moumouni na jam’iyar Moden Lumana da ‘yan adawa yace a dalilin wannan mahawara ya fahimci abubuwa da dama dangane da rawar da ya kamata ‘yan kasa su taka wajen tafiyar da lamuran kasa.
Yanayin da wannan mahawara ta gudana na nuna alamu bangarorin siyasar wannan kasa sun fara samun sassaucin ra’ayi idan aka kwatanta da yadda a shekarun baya dangantaka ta yi tsami a tsakanin ‘yan adawa da masu mulki a wani lokacin da ake matukar bukatar hadin kan ‘yan kasa domin tunkarar manyan kalubale irin su matsalar tsaro da sauransu.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5