: Hukumar zaben jamhuriyar Nijer ta bayyana shirin fara ayyukan rajistar ‘yan kasar mazauna ketare daga ranar 16 ga watan Yunin da ke tafe a ci gaba da shirye-shiryen zaben cike gurbin da zai bada damar aika mutanen da zasu wakilce su a majalisar dokokin kasar ta Nijar.
Tun a ranar 27 ga watan disamban 2020 ne ya kamata ‘yan Nijer mazauna kasashen waje su halarci runfunan zabe don kada kuri’a a zaben ‘yan majalisar dokoki da zagayen farko na zaben shugaban kasa, wato dai rana da daukacin ‘yan kasar dake zaune a gida sai dai hakan ba ta samu ba sakamakon anobar coronar da ake fama da ita a wancan lokaci.
Kasancewar a yanzu galibin kasashe sun bude iyakokinsu saboda alamun samun saukin wannan annoba ya sa hukumar zabe ta kasa CENI ta dauri aniyar soma rajistar ‘yan Nijer mazauna ketare da suka cancanci kada kuri’u . Dr Aladoua Amada shine matemakin shugaban hukumar zabe ta kasa CENI.
Kasashe 15 ne aka tantance domin shirya wannan zabe a bisa la’akari da wasu mahimman sharuda.
A shekarar 2016 ne ‘yan Nijer mazauna kasashen waje suka fara kada kuri’u a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki abinda ke basu damar aiko da wakilai 5 a majalisar dokokin kasar mai kujeru 171.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5