NIJAR: Gwamnati Na Kokarin Magance Tsadar Aikin Hajji

Hajji

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bayyana damuwa a game da abinda ta kira tsadar kujerar hajji sakamakon yadda ejoji ke son cin kazamar riba a cewarta, zargin da tuni suka yi watsi da shi.

NIAMEY, NIGER - A yayin wani taron da ya hada shugabanin ‘yan kasuwa da mambobin gwamnatin Nijar a karshen makon jiya ne Firai Minista Ouhoumoudou Mahamadou ya bayyana matsayin hukumomin Nijar a game da yanayin tafiyar da tsare tsaren haji da umara a kasar inda bayanai ke nunin dalilan kasuwanci na kokarin samun rinjaye fiye da sauran dalilan da su ka girka wannan fanni.

Sai dai kakakin kungiyar kamfanonin aikin haji da umara ta ANAP Alhaji Hassan Mani na cewa ma’aikata ba su yi wa shugaban gwamnati bayani akan gaskiya ba.

Firai minista ya tabo wata matsalar ta daban da maniyata suka jima suna kokawa akanta.

Ku Duba Wannan Ma Saudiyya Ta Bude Koffofinta Ga Duniya Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana

A nan kakakin kungiyar ejoji ta ANAP yace an sami canjin al’amura fiye da yadda aka sani a shekarun baya.

A nan gaba ne hukumar alhazai ta kasa wato COHO za ta fara zama da kungiyoyin ejoji ko kuma masu kamfanonin haji da umara don fara shirin wadannan ayyuka a bana idan hukumomin Saudia ba su canza matsayi ba a game da shirin bude masallatai don bai wa maniyata daga sassan duniya damar sauke farali a karon farko bayan da anobar coronavirus ta yi sanadin dakatar da al’amura a shekarar 2020.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Jama’a Na Kokawa Akan Kazamar Ribar Da Ake Ci Akan Kujerun Aikin Hajji A Nijar