NIJAR: Faransa Ta Soke Bizar Wani Fitaccen Mai Adawa Da Matakin Girke Sojojin Barkhane A Sahel

Shugaban kungiyar fafutuka ta Tounrons La Page Internatinale Maikoul Zodi

Shugaban kungiyar fafutuka ta Tounrons La Page Internatinale ya jaddada aniyar ci gaba da gwagwarmayar kare muradun kasashen Afirka bayan da ofishin jakadancin Faransa a birnin Yamai ya bada sanarwar soke takardar bizar da ke bashi izinin shiga kasar ta Faransa.

Koda yake ba a bayyana dalilan daukan wannan mataki ba, wasu na ganin abin tamkar na huce takaicin caccakar da yake yi wa manufofin shugaba Emammuel Macron.

A wata takarda da ya sanya wa hannu a ranar 20 ga watan Oktoba, jakadan Faransa a Nijar, Ambasada Sylvain Itte, ya sanar da shugaban kungiyar fafutuka ta Tournons La Page Internationale Maikoul Zodi matakin soke takardar bizar da ke ba shi izinin shiga kasar ta Faransa, abin da ke nufin daga yanzu ba shi da ‘yancin shiga kasar ballantana ya gudanar da wasu harkoki a kasar.

Da yake yi wa wata kafar kasarsa karin bayani jakada Sylvain ya ce ya lura Maikol Zodi ba ya zuwa Faransa akai-akai, saboda haka ya yanke shawarar soke masa biza.

A hirar shi da Muryar Amurka, Maikoul Zodi ya ce lallai da maraicen jiya Alhamis ya samu wannan takardar da aka ce masa an soke bizar da aka bashi na shiga da fita zuwa Faransa, sun ce wannan biza ta shekarar guda da yake da ita sun janyeta kuma idan yana son zuwa Faransa sai yazo wajensa idan yaga dama su bashi.

Zodi ya ce "ayyuka da Faransa ta ke yi ba daidai ba ne kamar a aiko sojojinsu suna zaune basa amfanin komai wannan muka ce bamu yarda da shi ba kuma wannan baya hana su ci gaba da wannan gwagwarmaya da suka saka a gaba don Nijar ta ci gaba ‘yan Sahel su samu ‘yancin kansu."

Shugaban kungiyar fafutuka ta Tounrons La Page Internatinale Maikoul Zodi

Sai dai wasu ‘yan Nijar na daukan wannan dambarwa a matsayin wani rikicin cikin gida wato tsakanin Faransa da wasu abokan tafiyarta na Jamhuriyar Nijar.

A nashi bayanin, shugaban kungiyar Mojen Siraji Issa ya ce Maikoul Zodi shine wanda hakika a shekaru biyu da suka wuce kasar Faransa ta bashi lambar yabo bisa ga ayyuka wadanda ya yiwa Faransa kuma a wancan lokaci sun zarge shi da yin leken asirin kasarsu.

“Hakika yau idan suka hana shi shiga kasarsu sai su ce fada ne da ubangida da shi da yaronshi, mai baka tallafi da ka’idoji to idan akwai ka’idoji da baka cika ba to yana iya ya taka maka burki, ta yiwu shi Maikoul Zodi ya yi ba daidai ba,” in ji Issa.

A karshen makon jiya ma gwamnatin Faransa ta bada sanarwar haramta wa wata fitacciyar ‘yar rajin kare muradun Afirka ‘yar asalin kasar Switzerland da Cameroon Nathalie Yamb shiga kasar, saboda zarginta da tunzura jama’a tare da yada akidar nuna kyama ga Faransa dalili kenan ake ganin soke bizar takwaranta na Nijar Maikoul Zodi tamkar wani matakin taka burki ga masu nuna kin jinin manufofi da tsarin siyasar Faransa a Afirka.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Faransa Ta Soke Bizar Wani Fitaccen Mai Adawa Da Matakin Girke Sojojin Barkhane A Sahel