Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zangar Da 'Yan Fafutuka Ke Shirin Gudanarwa Ta Haddasa Mahawara A Nijar


Dandazon jama'ar da suka fita zanga zangar farko a Yamai, Jamhuriyar Nijar, bayan sakin shugabannin masu fafutuka
Dandazon jama'ar da suka fita zanga zangar farko a Yamai, Jamhuriyar Nijar, bayan sakin shugabannin masu fafutuka

A Jamhuriyar Nijar, wasu kungiyoyin fafutuka sun kudiri aniyyar gudanar da zanga zanga a ranar Lahadi 30 ga watan Janairu da nufin nuna rashin gamsuwa da yadda al’amura ke gudanar a kasar, misali yadda mahukunta suka gaza shayo kan matsalolin tsaron da suka addabi jama’a.

Sai dai wasu mukusantan gwamnatin ta Nijar na kallon abin tamkar wani yunkurin kwatanta abubuwan da suka faru a kasashe makwabta.

Sakin ragamar gudanar da zanga-zanga na daga cikin bukatun da shugabanin kungiyoyin fararen hula suka gabatar a yayin ganawarsu ta farkon watan nan da shugaban kasa Mohamed Bazoum.

Hakan shi ne mafarin kungiyoyin suka kudiri aniyyar fitowa tituna a ranar Lahadin dake tafe a wasu biranen kasarda nufin bayyana damuwarsu akan abubuwa na ba daidai ba da suka ce suna wakana kamar yadda Maikol Zody na kungiyar Tournons la Page ya bayyana.

Sai dai a cewar Tsayabou Lawan Salao na RODDHAD, wata kungiyar farar hular dake goyon bayan gwamnati, ba za a rasa wata ajandar boye ba bayan wannan zanga-zanga a bisa la’akkari da abubuwan da suka wakana a baya bayan nan a kasashe makwafka.

Amma Maikol Zody ya tabbatar da cewa ba su da irin wannan tunani da ya sabawa mulkin dimokradiya.

Shekaru sama da 3 kenan ake ce-ce-ku-ce game da rashin samun ‘yancin gudanar da zanga-zanga a nan Nijar inda hukumomi ke bayyana dalilan tsaro da na annobar corona a matsayin hujjojin hanawa kungiyoyin fararen hula shirya jerin gwano ko gangami da makamantansu.

Hakan ya sa aka yi ta safa da marwa a kotuna saboda yadda sau tari irin wannan haduwa ke rikidewa zuwa tarzoma.

Amma bayan gabatarwa shugaban Bazoum damuwarsu akan matakin hana zanga-zanga, shugaban ya ba su tabbacin kawo karshen wannan matsala muddin suka mutunta doka.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG