Nijer: Shirin Komawa Makaranta

Yayinda daliban jami’o’in Janhuriyar Nijer ke sa-ran komawa makaranta a makon gobe, kungiyar daliban jami’ar Abdulmumuni ta Yamai ta gargadi hukumomin ilimi mai zurfi su gaggauta magance matsalolin daliban.

Bisa wani sabon tsari da hukumomin ilimi mai zurfi suka bullo da shi a ranar 3 ga watan Satunba dake tafe ne ya kamata daliban jami’o’i su koma kan aji sai dai kungiyar UENUN ta daliban jami’ar Yamai wadda ta fitar da wata sanarwa na ganin zai yi wuya wannan kudirin ya tabbata saboda a cewar sakataren kungiyar Arifa Hassan har yanzu akwai tsangayar da dama da ba su kammala darussan shekarar 2017 zuwa 2018 ba.

Yanayin rayuwa da yanayin karatu na daga cikin batutuwan da daliban jami’ar Yamai suka bukaci gwamnati ta dauki matakai akansu don ganin karatu ya gudana cikin nutsuwa a tsawon shekara mai kamawa.

Ministan ilimi mai zurfi Yahouza Sadissou bayani akan wannan al’amarin ba to amma yace idan lokacin yin bayani ya yi zai kira taron manema labarai don bayyana matsayin gwamnati.

Takun saka tsakanin dalibai da hukumomin ilimi mai zurfi wani abu ne da ya matukar jijjiga sha’anin karatu a shekarar da ta gabata, lamarin da ya sa gwamnatin nijer jibge jami’an tsaro a jami’ar Yamai tare da rufe wuraren kwanan dalibai a wasu jami’o’in kasar da nufin yayyafa ruwa akan wutar rikicin da ta samo asali daga matakin korar wasu shugabannin kungiyar UENUN daga jami’ar ta Yamai saboda zarginsu da dukan wani malaminsu.