Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Da Kamaru Sun Yi Taron Fadakar Da Juna


Al’ummomi yan asalin yankin Najeriya da Kamaru da kasar Burtaniya ta mulka da ake kira "yan amana',sun soma tarukan bita da kuma fadakar da juna a Najeriya,biyo bayan taron da suka gudanar a Bamenda,na Kamaru domin tunawa Najeriya da kasar Kamaru irin yarjejeniyoyin da aka kulla da majalisar dinkin duniya a shekarun baya.

A Najeriya dai kusan kananan hukumomi 16 ne na jihohi biyar ke cikin wannan batu kuma wadannan yankuna sun hada da yankin kananan hukumomin Mubi ta arewa da Mubi ta kudu, sai karamar hukumar Toungo, da Ganye da kuma kananan hukumomin Gashaka, Kurmi, Sardauna na jihar Taraba.

Mrs Tiyasa Agustine na cikin matan da suka hallarci wannan gangami daga Ganye, tace zasu cigaba har sai hakarsu ta cimma ruwa.

A sakonsa ga mahalarta taron shugaban wannan fafutukar Farfesa Martin Chia Ateh,wanda har ila yau yake wa majalisar dinkin duniya aiki a matsayin jami’in tuntuba ta fannin diflomasiya, cewa yayi ‘’Dole a cigaba da fadakar da al’umma,tunda ba tun yau ba kotun duniya ta bada hukunci kan lamarin kuma duk kasashen da abun ya shafa sun sani har yana cikin taswirar duniya.Wasu yan abubuwa kadan wato technicality ne suka rage,’’ da sannu za’a kai ga cimma ruwa.

Saurari rahoton Ibrahim Abdul'aziz

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG