Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyun Adawan Sudan ta Kudu Sun Ki Amincewa Da Sabuwar Yarjejeniya


Matan Sudan ta Kudu suna zanga zangar neman zaman a kasarsu
Matan Sudan ta Kudu suna zanga zangar neman zaman a kasarsu

Madugun 'yan adawan Sudan ta Kudu Riek Machar da sauran jam'yyun adawa sun ki amincewa da sabuwar yarjejeniya saboda haka ba su rabtaba hannu a kai ba.

Shugaban ‘yan adawa a Sudan ta Kudu, Riek Machar da sauran jam’iyyun adawan kasar, sun ki amincewa su rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar da aka farfado da ita, domin kawo karshen yakin basasan kasar da aka kwashe shekaru biyar ana yi.

A watan da ya gabata, Machar da shugaba Salva Kiir suka rattaba hannu akan wata matsaya ta tsagaita wuta da kuma wata yarjejeniya kan yadda za a raba mukamai a tattaunawar da suka yi a Khartoum, amma ba tare da an cimma matsaya kan adadin jihohi da kuma iyakokinsu ba, batun da ya zamanto mai cike da takaddama.

Daya daga cikin wakilan da suka halarci zaman tattaunawar a jiya Litinin, ya tabbatar da cewa an mika wannan batu ga shugabannin kasashen hukumar gwamnatocin raya kasashen yankin da aka fi sani da IGAD a takaice, domin su yanke shawara.

Wata mamba a gamayyar kungiyoyin matan Sudan ta Kudu, Rita Lopidia, ta ce bayan da aka koma kan teburin tattaunawa a karshen makon da ya gabata, bangarorin sun gaza cimma matsaya kan sashe na 4 a wannan yarjejeniya ta 2015 da aka farfado da ita, saboda kowanensu, ya jajirce kan matsayar da ya dauka kan adadin jihohi da iyakokinsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG