Niger Da Nigeria Suna Sintirin Hadin Gwiwa Akan Iyakarsu.

Ministan tsaron Jamhuriyar Niger Kalla Mountari

Nigeria da Jamhuriyar Niger sun hada gwiwa domin yaki da yadda ‘yan bindiga ke neman mayar da jihar Maradi a jamhuriyar Niger da jihar Zamfara a Nigeria wuraren aiwatar da muggan dabi’u

Hukumomin tsaron jamhuriyar Niger sun bayyana kara karfafa matakan tsaro akan iyakar jihar Maradi da ta Zamfara a tarayyar Nigeria bayan da aka gano alamar masu satar mutane domin neman kudin fansa na kokarin samun gindin zama da nufin gujewa samamen da sojojin Nigeria suka kaddamar a jihar Zamfara mai fama da ‘yan bindiga.

Ministan tsaron kasar Niger Kalla Moutari ya bukaci hadin kan talakkawa domin murkushe wannan bakon al’amari.

Ministan ya ce yau ana iya a sace mutum daga wannan bangaren zuwa wancan kana a kira ‘yanuwansa su biya kudin fansa. A saboda haka ya yi kira ga duk jami’an tsaron kasar ta Niger su hada kai su yi maganin wannan sabon salon sata dake neman gidin zama a kasar.

Mahukumtan Niger na son jami’an tsaro su fito da tsarin da zasu bi su shawo kan lamarin cikin dan lokaci kadan. Dole su dauki hanyoyin da zasu murkushe wanna bakar sana’ar cutar da jama’a

Ministan ya ce tuni aka hada kai tsakanin jami’n tsaron kasar sa dana Nigeria, kuma tare suke sintiri akan iyakokinsu. Duk wanda ya karya dokar Niger ya tsere zuwa Nigeeia za su kamoshi su hukumtashi a Niger. Haka ma Nigeria ta na iya shiga Niger ta zakulo duk wanda ya yi aika aika a jihar Zamfara. An dauki wannan matakin da nufin samu hadin kan yakar muggan mutanen koina suke tare da zakulo masu daure masu gindi a hukuntasu.

A saurari hirar Souley Barma da Minista Kalla Moutari

Your browser doesn’t support HTML5

Niger Da Nigeria Na Sintiri Kan Iyakarsu Tsakanin Maradi Da Zamfara - 2' 25"