JIHAR NIGER: An Yi Taron Fadakar Da Matasa Akan Illar Shiga Bangar Siyasa

Taron wasu matasan jihar Neja

Wata kungiya a jihar Neja ta gudanar da taron fadakar da matasa akan illar shiga bangar siyasa tare da jaddada muhimmancin zaman lafiya.

Masu ruwa da tsaki akan siyasa a jihar Neja sun dukufa wajen fadakar da matasan jihar domin kaucewa shiga ko haddasa rikicin siyasa.

Ana kokarin taimakawa matasa su fahimci illar shiga bangar siyasa da rikicin da furta kalamun batanci ka iya jawowa kan zaman lafiya.

Ta dalilin haka ne wata kungiyar matasa ta gudanar da wani babban taron fadakar da matasan a garin Bida, birni da a kwanakin baya wasu matasan suka yiwa tawagar gwamnan jihar ature.

Muhammad Isa Isange, shugaban kungiyar da ta shirya taron, ya ce abubuwan da suka faru da gwamnan kwanakin baya a cikin garin Bida ba abun da suka so ba ne. Yaci gaba d a cewa tun lokacin da lamarin ya faru manyan yankinsu suka tashi tsaye, suka kira matasan suka yi masu kashedi tare da fada masu abun da ya kamata su yi.

Malam Muhammad ya gargesu akan su daina shaye-shayen abubuwan dake haddasa maye. Ya ce manyansu a garuruwa kamar Lapai, Mokwa da dai sauransu suna zama da matasan, suna fadakar dasu akan muhimmancin zaman lafiya.

Injiniya Muhammad Daban, wanda ya kasance jigo ne a jam'iyyar APC mai mulki da ya halarci taron, ya bayyana muhimmancin shirya irin taron a daidai wannan lokacin da zaben 2019 ke karatowa. Ya ce ba ddai-dai bane 'ya'yansu su rika yin abubuwan kamar lokacin jahiliya. Maimakon haka Injiniya Daban yace, kamata ya yi su kasance masu tarbiya da natsuwa saboda yanzu matashi na iya zama shugaban kasa.

Jami'in yada labarai na gwamnan jihar Jibril Baba Ndaci, ya ce ko baya ga fadakar da matasan ana iya yin anfani da taron wajen fadakar da mutane akan ayyukan da gwamnati ta gudanar domin anfanin jama'a.

Daga karshe mahalarta taron sun amince da sake tsayawar gwamnan takara a zaben shekarar 2019.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

NIGER: An Yi Taron Fadakar Da Matasa Akan Illar Shiga Bangar Siyasa - 2' 43"