A jiya Lahadi hukumomin kasar New Zealand, sun fara mayar da wasu daga cikin mutane 50 da aka yi wa kisan gilla ranar jumma’a a wasu masallatai biyu ga iyalansu don su yi kokarin binne su kamar yadda Musulunci ya tanada.
Firaiministan Jacinda Ardern ta ce nan da ranar Laraba za a kammala mika gawarwakin ga iyalansu.
Ta kuma ce wasu kwararru shida sun shigo kasar daga Australia domin su taimaka a kokarin da ake na gano wadanda suka mutu.
Shugabar masu binciken musabbabin mutuwa, Deborah Marshall, ta ce ofishinta “ya himmatu a yyukan da yake yi” domin ya tabbatar da an mika kowacce gawa ga ‘yan uwanta, inda ta kara da cewa “babu abu mafi muni, a ce an ba wani iyali gawar da ba ta shi ba.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Wally Haumaha, ya fada jiya Lahadi cewa, ofishinsa ya hadu da shugabannin al’umar Musulmai don su fahimtar da su irin dogon lokacin da ake dauka idan ana binciken musabbabin mutuwa, musamman kan wani babban laifi kamar wannan.