Mutumin nan da aka fi zargi a harbe-harben kan mai uwa da wabi a wasu masallatai biyu a garin Christchurch na kasar New Zealand, inda har mutane 49 su ka mutu, ya gurfana gaban kotu a yau dinnan Asabar.
Brenton Tarrant dan shekaru 28 dan asalin kasar Australia, wanda ya amsa cewa shi mai tsattsauran ra’ayin fifita fararen fata ne, wasu dogarawan tsaron kotu ne su biyu dauke da manyan makamai, suka taso keyarsa zuwa kotun garin Christchurch, inda wani alkali ya karanta masa tuhumar kisa da ake masa.
Bayan da wanda ake zargin ya fice daga kotun, sai alkalin ya ce, “A yayin da mutum daya ake zargi zuwa yanzu, ba zai saba hankali ba idan aka kyautata zaton cewa za a samu karin wadanda ake zargi daga baya.”
Hasali ma an damke wasu wasu mutane biyu masu alaka da shi. ‘Yansanda na kokarin tantance irin rawar da mutanen su ka taka, idan akwai hannunsa.
A wani taron manema labarai da ta kira da safiyar yau dinnan Asabar, Firaministar New Zealand Jacinda Arden ta kara da yin alkawarin cewa, “Za mu canza dokokin mallakar bindiga,” Ta ce mutumin da ya aikata kashe-kashen, ya na dauke da bindigogi biyar, da wasu bindigogi na musamman masu sarrafa kansu biyu, kuma ya mallake su ne ta hanyar doka.
Firaministan Australia Scott Morrison, ya tabbatar cewa mutumin da ake zargin dan asalin kasar Australia ne, kuma ya ce mutumin “wani dan ta’adda ne mai tsattsauran ra’ayin rikau.”
Facebook Forum