Netanyahu Ya Amince Da Sabuwar Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza

Firai Ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu

Firai Ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya amince da sabon zagayen tattaunawa game da tsagaita bude wuta a Gaza su gudana a biranen Doha da Alqahira, a cewar sanarwar da ofishinsa ya fitar a yau Juma'a, kwanaki bayan da ake ganin kamar tattaunawar ta cije.

WASHINGTON DC - Tun bayan da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da kudirin neman a gaggauta tsagaita wuta a Gaza a Litinin din data gabata, Isra"ila da kungiyar Hamas ke zargin juna da gazawa wajen cimma yarjejeniyar.

A Talatar data gabata, mai shiga tsakani kasar Qatar tace ana cigaba da tattaunawa tsakanin Hamas da Isra'ila akan tsagaita wuta a Gaza tare da sakin mutanen da ake garkuwa dasu, saidai dukkanin bangarorin dake rikici da juna da mai shiga tsakanin basu yi karin haske game da lamarin ba.

Ofishin Netanyahu ya ce firimiyansa ya zanta da shugaban hukumar leken asirin Isra'ila, Mossad, David Damea game da tattaunawar sulhun, saidai ba'a bayyana ko bamea din zai yi balaguro zuwa biranen Doha da Alqahira domin halartar tattaunawar ba.

Yaki ya barke tun bayan da Hamas ta kaddamar da wani hari da ba'a taba ganin irinsa ba, wanda yayi sanadiyar asarar rayuka 1, 160, galibinsu farar hula, a cewar kididdugar gwamnatin Isra'ila da kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.

A cewar ma'aikatar lafiya dake karkashin gudanarwar kungiyar Hamas, Isra'ila ta kaddamar da harin ramuwar gayyar akan Hamas wanda yayi sanadiyar asarar rayuka mazauna yankin Gaza dubu 32 da 623 galibinsu mata da kananan yara.

Falasdinawa masu fafutuka da makamai sun yi garkuwa da Yahudawa da baki 'yan kasashen ketare 250 a yayin harin da aka kaiwa isra'ila na ranar 7 ga watan Oktoban daya gabata, saidai an saki da dama yayin tsagaita wutar mako guda da aka yi a watan Nuwambar daya gabata.

Isra'ila ta hakikance cewar akwai sauran kimanin mutane 130 da ake garkuwa dasu a Gaza, ciki harda mutum 33 da ake zaton sun mutu; sojoji 8 da farar hula 25.