Wannan wata muhimmiyar ci gaba ce a shari’ar dake zuwa a daidai lokacin da shugaban ke fuskantar yaki a Gaza tare da sammaci daga kotun duniya akan tuhume-tuhumen aikata laifuffukan yaki.
A cikin kasarsa kuma, Netanyahu na fuskantar shari’a akan zarge-zargen zamba da cin amana da karbar rashawa a wasu al’amura 3. Netanyahu ya musanta zargin aikata ba dai dai ba, sai dai gurfanarsa a gaban kotu tawaye ce a tsawon shekarun daya shafe yana siyasa, wacce ta saba da kimar kasaitaccen shugaba mai mutunci da yake kokarin nunawa.
Shari’ar za ta cinye wani gwaggwaban kaso na lokacin Netanyahu a wannan lokaci mai matukar mahimmanci ga Isra’ila. Yayin da zai shafe makonni yana fuskantar shari’a, za’a bukace shi ya ci gaba da tasrifin al’amura a yakin Gaza da kula da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsa da kungiyar mayakan Hezbullahi ta Lebanon da kuma sa idanu akan barazanar dake fitowa daga kasashen Gabas ta Tsakiya, ciki har da Iran.
Wannan ne zai zama karon farko da wani Firai Ministan Isra’ila zai gurfana a gaban kotu a bisa tuhumar aikata laifi, kuma sau da dama Netanyahu ya yi ta janyo tsaiko a shari’ar, yana fakewa da yakin Gaza da matsalolin tsaro.
Alkalan kotun sun bada umarnin a cigaba da shari’ar a gobe Talata, inda suka mayar da sauraron karar zuwa wata kotun karkashin kasa dake birnin Tel Aviv a matsayin matakin tsaro.
-AP