NEPAL: An Zakulo Dan Shekara 101 da Ransa Bayan Kwanaki Takwas

Masu aikin ceto a Nepal

A wani abun alajabi masu aikin ceto a Nepal sun zakulo wasu mutane uku da ransu har da wani dan shekara 101.

An kara samo wasu mutane 4 daga baraguzan rusassun gine-gine da ransu, kwanaki da yawa bayan muguwar girgizar kasar da aka yi a Nepal, ciki har da wani mai shekaru 101 da haihuwa.

‘Yan Sanda sun fada a jiya Lahadi cewar an samo wani mutum kilomita 80 daga arewa maso yammacin babban birnin kasar Kathamandu.

Ma’aikatan agaji dai sun fitar da rahotanceto mutanen guda 3 a garin Sindhupalchowk dake yankin arewa maso gabashin birnin Kathma.

Amma jami’ai sunce kwanaki takwas bayan girgizar kasar, tsammanin samun ceto wasu mutane na gushewa, kuma adadin mutanen da suka mutu zai hauradubu 7 da aka yi kiyasi a halin yanzu.

Har yanzu ba’a san inda dubban mutane suke ba, ciki harda mutane dubu ‘daya da suka je kasar ziyara daga turai.