A Nepal Majalisar Dinkin Duniya tace ta fara rarraba abinci da magunguna a wurin dake kusa da inda girgizar kasar da ta ratsa kasar ranar Asabar ta samo asali, inda har yanzu adadin wadanda bala'in ya rutsa dasu yake haurawa.
Kokarin da hukumar cimaka ta Majalisar Dinkin Duniya take yi a kewayen wurin da ake kira Gorkha yazo ne a dai dai lokacinda jami'an kasar suke alkwarin cewa jama'a zasu ga canji kan yadda gwamnati zata yi aikin samar da taimakon abinci da ruwa da kuma matsuguni.
Ahalinda ake ciki kuma, masu aikin ceto suna ci gaba da tonon baraguzan gine gine da girgizar kasar mai kafin awo 7.8 ta rusa. A daren Talata wata tawagar masu aikin ceto daga Faransa sun zakulo wani mutum da rai daga baraguzan gidansa da ya rushe a Kathmandu babban birnin kasar tun ranar Asabar.