Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NEPAL: An Sake Zakulo Wasu Mutane Da Ransu


Wani gini a Nepal kenan da ya ruguje sanadiyyar girgizar kasar.
Wani gini a Nepal kenan da ya ruguje sanadiyyar girgizar kasar.

An zakulo wasu mutane 3 daga cikin bangorin rusassun gine-gine da ransu, kwanaki takwas bayan gagarumar girgizar kasar da aka yi a Nepal.

Jami’an sojoji da na ‘yan sanda ne suka ceto mutanen guda 2 maza da mace 1 a garin Sindhupalhowk da ke yankin arewa maso gabashin birnin Kathma.

Jami’an dai suna cewa zai yi wuya a sake ganin wasu da zasu tsira a cikin bangoran gine-ginen. Ma’aikatar cikin gida ta Nepal tace wadanda suka mutu sun haura mutum 7000, a yayi da dubbai suka bace ciki har da ‘yan kasashen Turawa kusan 1000.

Wadanda suka tsira da rayuwarsu suna ta roko ga gwamnati da kungiyoyin agaji da su gaggauta basu agajin abinci, ruwan sha da sauran kayan agaji garesu da da dama suka rasa muhallansu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG